An ƙarfafa Rundunar ‘Yan Sandan Kano da kayan aiki don zaɓe mai zuwa

Daga RABIU SANUSI a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta samu ƙarin motocin gudanar da aiki da sauran kayan kariya yayin gudanar da zaɓen gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi daga hedikwatar rundunar da ke Abuja.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwar manema labarai da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya fitar ranar Laraba.

Sanarwar ta ce kayayyakin da rundunar ta karɓa sun haɗa da motocin kariya, bindigar harba barkonon tsohuwa da sauransu.

Ya ce sn ba da kayan ne dan ci gaba da gudanar da aiki yadda ya kamata musamman a lokacin zaɓen nan da ke tafe.

Kazalika, Kiyawa ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Mamman Dauda, ya ce yana mai taya Shugaban ‘Yan Sandan na Ƙasa, Usman Alkali Baba, murna da godiya bisa jajircewar da yake yi wajen ganin an samu kyakkyawan tsaro a faɗin ƙasar nan.

Kiyawa ya bayyana irin ƙoƙari da hoɓasar rundunar ‘yan sandan Kano wajen shirya tarurrukan ƙara wa juna sani da tattauna yadda za a daƙile duk wata hanyar ɓarna.

Haka nan, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano tare da masarautun jihar da ma al’ummarta dangane da goyon bayan da suke ba wa ‘yan sanda wajen gudanar da harkokinsu a jihar.

A ƙarshe, jami’in ya yi kira ga ‘yan siyasa a jihar da su guji amfani da ‘yan daba wajen tada ƙayar baya yayin gudanar da zaɓe da bayan zaɓen.

Kana ya ba da wasu lambobin waya wanda za a yi amfani da su wajen tuntunɓarsu domin kwarmata musu abin da ke faruwa wanda ba daidai ba a faɗin jihar: 08032419754, 09029292926, 08123821575.