An ƙaryata rasuwar Raiola

Daga MAHDI M. MUSA

A halin da ake cikin yanzu, Mino Raiola dai yana fafutukar neman lafiyarsa ne a asibiti, inda wakilin ƙwallon ƙafar ya yi kakkausar suka ga labaran ƙarya da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta na cewa ya mutu.

Raiola yana wakiltar manyan mutane marasa adadi a manyan wasannin Turai kuma ya taimaka wajen ƙulla manyan yarjejeniyoyin da suka haɗa da Paul Pogba da Zlatan Ibrahimovic.

An ruwaito cewa, ɗan ƙasar Italiyan ya rasu yana da shekaru 54 a duniya, inda Raiola ya fitar da wata sanarwa a dandalinsa na sada zumunta inda ya nuna rashin jin daɗinsa da labarin na ƙarya.

Raiola ya aike da salo ga mabiyansa a shafinsa na Tuwita a daidai lokacin da ake ta cece-ku-ce game da lafiyarsa, inda ya ce, “a halin da ake ciki yanzu na rashin lafiyata abin mamaki ne, amma mutane na neman kashe ni ban mutu kawai don na yi fama da rashin lafiya karo biyu a cikin watanni 4”.

A halin da ake ciki, babban abokin Raiola, Jose Fortes Rodriguez ya soki rahotannin mutuwarsa, inda ya shaida wa De Telegraaf cewa, “Mino bai mutu ba. Waɗannan rahotannin banza ne.”

Likita Alberto Zangrillo daga Asibitin San Raffaele da ke Milan ya ƙara da cewa, “na yi matuƙar fusata da kiran wayar da wasu ‘yan jarida na bogi ke yi na hasashe kan rayuwar wani mutum da ke neman lafiya.”

Raiola ya wakilci ‘yan wasan Italiya biyu Mario Balotelli da Marco Verratti shima, da kuma sabon ɗan wasan Ajax Ryan Gravenberch da Denzel Dumfries na Inter.