An ƙone matashiyar da ake zargi da ɓatanci ga Annabi a Sakkwato

-A kai zuciya nesa, cewar Majalisar Sarkin Musulmi
-Mun rufe kwalejin har illa masha Allahu – Gwamnati
-’Yan sanda sun kama mutum biyu

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Matasa sun ƙone wata matashiya da ake zargi da yin ɓatanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (SAW), a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, lamarin da ya tilasta wa gwamnati rufe kwalejin ba tare da bayyana ranar da za a koma karatu ba.

Ɗaruruwan ɗalibai da wasu mata sun gudanar da zanga-zanga tare da ciro wacce ake zargin daga maɓoyar da hukumomin makaranta suka ɓoye ta, inda suka kashe tare da ƙone gawar tata.

Sai dai a bayanin da Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta fitar kan lamarin mai ɗauke da sa hannun Sakataren Majalisar, Alhaji Sa’idu Muhammad Maccido (Ɗanburan Sakkwato), majalisar ta nuna rashin jin daɗinta kan faruwar lamarin a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato.

“Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta yi Allah wadai da abubuwan da suka faru a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari dake Sakkwato, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar ɗalibar kwalejin,” a cewar sanarwar majalisar.

Bisa wannan ne majalisar ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankulansu tare da cigaba da wanzar da zaman lafiya a jiha da ƙasa bakiɗaya.

A yayin da ya ke mayar da jawabi ga manema labarai, Kwamishinan Ma’aikatar Yaɗa Labara na Jihar Sakkwato, Alhaji Isa Bajini Galadanci, a taron da ya gudanar da su a madadin gwamnatin jihar, kwamishinan ya bayyana cewa, gwamnatin ta bayar da umarnin rufe kwalejin tare da umartar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta yi bincike tare da jami’an tsaro dangane da lamarin.

“Tuni dai Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya umurci Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da hukumomin tsaro da su gudanar da binciken musabbabin faruwar lamarin tare da gabatar da sakamakon rahoton bincike ga gwamnati,” inji kwamishinan.

Baya ga umurnin rufe kwalejin nan take da gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankulansu tare da zama lafiya, domin gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace bayan karvar rahoton binciken lamarin daga hukumomi.

Haka zalika Rundunar ’Yan Aandan Jihar Sakkwato ta bakin Kakakinta, ASP Sanusi Abubakar, a sanarwar da ta fitar, ta bayyana cewa, tuni dai ta soma gudanar da bincike kan lamarin wanda tuni ma ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin.

“Da misalin qarfe 9:00 na safiya Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sakkwato ta samu kira daga Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari cewa, ɗaliban kwalejin sun soma zanga-zanga bisa wata ɗalibar kwalejin mai mataki na biyu, Deborah Samuel, da ake zargi da yin kalaman vatanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), wanda ɗaliban suka fito da ɗalibar daga mavoyar da hukumar makarantar suka ɓoye ta, inda suka kashe ta tare da banka wa gawar ta wuta.”

A cewar rundunar dai, jim kaɗan da samun labarin, rundunar ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen zuwa kwalejin domin daidaitar lamurra, kuma duk da cewa an rufe kwalejin kakakin ya ce jami’an nasu na nan jibge a kwalejin har ya zuwa yanzu.

“Kwamishinan ‘Yan Aanda na Jiha, CP Kamaluddeen Kola Okunlola, yana kira ga al’umma su kasance masu bin doka da oda, kana kada su ji wani fargaba kasantuwar rundunar ta su tana ƙoƙarin wajen daidaita lamarin,” a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *