An ɗauke wuta a Fadar Shugaban Ƙasa da wasu sassan Abuja bayan sace wayoyin layukan lantarki

Daga BELLO A. BABAJI

Fadar shugaban ƙasa dake Abuja da ake kira da Aso Rock ta shiga halin ɗaukewar wuta bayan da wasu ɓata-gari suka sace wayoyin layukan lantarkin da ke kai wa fadar da wasu sassan birnin wuta.

Babban jami’in yaɗa labaran Kamfanin Raba Wutar lantarki ta Ƙasa (TCN), Ndidi Mbah ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a inda ya ce lamarin ya auku ne a yankin wajen shaƙatawa na ‘Millennium Park’.

Jami’in ya kuma ce ɓarayin sun kuma ɗauke waya mai tsawon mita 40 wanda hakan ya shafi ɓangarori takwas na yankin Central Area, kuma ya shafi kaso 60 na wutar lantarkin Abuja.

Sauran yankunan da lamarin ya shafa sun haɗa da Maitama, Wuse Jabi, LifeCamp, Asokoro, Utako da Mabushi, sakamakon sace wayoyin ƙasa da ke raba wuta ga yankunan a rumbun dake Katampe.

Ya kuma bayyana damuwa kan yadda lalata layukan lantarki ya zama ruwan dare a sassan Nijeriya, ya na mai cewa tuni TCN ya tura injiniyoyi domin gyara wuraren da lamarin ya shafa.