An ɗaura auren Jarumar Kannywood, Aisha Tsamiya, bayan canjin waje da lokaci

Daga WAKILINMU

A jiya Juma’a aka ɗaura auren jarumar Kannywood, Aisha Muhammad Ali, da aka fi sani da Aisha Tsamiya, tare da agonta Alh Buba Abubakar.

An ɗaura auren ne kamar yadda aka tsara, sai dai an samu sauyin wajen ɗaurin auren da kuma lokaci saboda dalilai na tsaro.

Bayanan da Blueprint Manhaja ta kalato sun nuna an samu sauyin wuri da kuma lokacin ɗaurin auren ne kasancewar angon babban mutum ne sananne, haka ma amaryar fitacciyar jaruma ce wadda ke da ɗimbin masoya, wanda hakan ya sa aka ɗauki matakin sauyin don kauce wa duk matsalar da ka iya tasowa.

An dai ɗaura auren ne da safe saɓanin yadda tsarin yake da farko a kan sai bayan an sauko daga Sallar Juma’a ba za a ɗaura. Haka nan, an ɗaura ne a Masallacin Malam Aminu Ibrahim Daurawa a maimakon Masallacin Juma’a na Zarban da ke ‘Yan Kaba kamar yadda katin gayyata ya nuna tun farko.

Da alama dai rahoton da ya karaɗe kafafen yaɗa labarai a ranar jajibirin auren inda aka rawaito amaryar ta kore cewa ba Juma’ar za a ɗaura aurenta ba, wani salo ne na ɓadda sawu don kauce wa duk wata matsalar da ka iya faruwa saboda cinkoson jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *