An ɗaure lauya bisa tafka ƙarya a gaban kotu

Mai shari’a Mojisola Dada ta kotun hukunta manyan laifuka da ke zama a Ikeja a Jihar Legas ta ɗaure wani lauya Kenneth Ajoku hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari tare da zaɓin biyan tara bisa laifukan ƙarya da kuma ƙirƙirar shaidar ƙarya.

Alƙalin kotun ta kama shi da laifuka biyu a cikin wasu tuhume-tuhume biyun da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta ke yi a kansa.

Rahotanni sun bayyana cewa, an fara tuhumar Ajoku ne tun a shekarar 2017 lokacin da hukumar EFCC ta samu bayanan sirri game da gungun ’yan damfara da ke sayar da kadarorin gwamnatin tarayya.

Bayan bincike cikin tsanaki, EFCC ta ce, an gayyaci Ajoku da tawagarsa zuwa hukumar, amma ya ƙi zuwa yayin da aka buƙaci ganinsa a lokuta daban-daban.

Jami’an hukumar sun ziyarci ofishin wanda ake tuhuma, amma ba a same shi ba. A wani yunƙuri na kawo cikas ga binciken, Ajoku ya tunkari alƙalin babbar kotun tarayya da ke Ikoyi, Legas, Ibrahim Buba, domin ya rantse da cewa jami’an hukumar sun kama shi tare da tsare shi a ranar 4 ga Mayu, 2017. Ya kuma buƙaci a biya shi diyyar Naira miliyan 300. Kotun dai ta ƙi amincewa da buƙatar ta kuma umarce shi da ya gabatar da kansa domin binciken hukumar EFCC.

Daga nan sai ya garzaya zuwa kotun ɗaukaka ƙara da ke Legas, a wani mataki na dakatar da binciken da hukumar EFCC ke yi a kansa. Kotun ɗaukaka ƙara ita ma ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar.

Daga nan aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume biyu da suka haɗa da ƙarya da ƙirƙirar shaidun ƙarya, wanda aka ce ya saɓa wa sashe na 85(1) 86(1) da 88(1) na dokokin laifuka na Jihar Legas, 2011.

Ya musanta tuhumar da EFCC ta ke yi masa, sannan aka ci gaba da shari’ar gaba ɗaya. A yayin shari’ar, lauyan masu shigar da ƙara, Franklin Ofoma, ya kira shaidu uku tare da gabatar da wasu takardu da kotun ta amince da su a gabanta. Da take yanke hukunci a ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba, 2021, Dada ta kama shi da laifuka biyu, sannan ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari, tare da zaɓin tarar Naira miliyan 2.5.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *