An ƙaddamar da gadar Foundiougne da kamfanin Sin ya gina a Senegal

Daga CMG HAUSA

Jiya Asabar 26 ga wata, shugaban ƙasar Senegal Macky Sall, ya halarci bikin ƙaddamar da babbar gadar Foundiougne da kamfanin ƙasar Sin ya gina ta hanyar rancen kuɗin da ƙasar ta nema daga ƙasar Sin.

Kamfanin ƙasar Sin ya fara aikin gina gadar tun shekaru uku da suka gabata, yanzu haka gadar ta fara aiki a hukumance.

Shugaban ƙasar Senegal da magajin birnin Foundiougne da jakadan ƙasar Sin dake ƙasar da wasu wakilan kamfanin ƙasar Sin sun halarci bikin, inda shugaban ƙasar Sall ya yanka ƙyalle domin bude gadar.

Babbar gadar mai tsayin mita 1600 tana birnin Foundiougne dake yamma maso tsakiyar ƙasar Senegal, wadda ke ketare kogin Saloum, a halin yanzu gadar ta kasance mafi tsayi a ƙasar wadda ke ketaren kogi, kuma aikin gina gadar ɗaya ne daga cikin manyan ayyukan da ake gudanarwa bisa “shirin farfado da Senegal”, kana wani ƙoƙari ne da kasar Sin ke yi domin tabbatar da ayyukan haɗin gwiwa goma ƙarƙashin hulɗar Sin da ƙasashen Afirka.

Fassarawa: Jamila