An ƙaddamar da layin dogo na farko a Masar wanda kamfanin Sin ya gina

Daga CMG HAUSA

A Jiya Lahadi ne aka ƙaddamar da wani layin dogo na jirgin ƙasa a ƙasar Masar, wanda kamfanin Sin ya gina, kuma ya kasance hanyar jiragen ƙasa ta farko dake amfani da wutar lantarki a Masar.

Shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi, da firayin minista Mostafa Madbouly, da sauran jamian Masar, da jakadan Sin dake Masar Liao Liqiang sun halarci bikin gwada layin dogon, inda suka isa tashar Badr daga tashar Adly Mansour ta jirgin ƙasa.

Yayin ƙaddamarwar, ministan sufuri na Masar Kamel el-Wazir ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, kashi na farko na aikin gwajin hanyar zai gudana ne ta amfani da taragun jiragen ƙasa 22, ana kuma hasashen cewa, za a iya yin jigilar fasinjoji 360,000 a duk rana.

Liao Liqiang ya nuna cewa, ɓangaren Sin ya samar da kudi da fasahohin da injunan Sin ga wannan aikin layin dogo da ake kiran shi “10th of Ramadan City, yayin da kamfanonin Sin da na Masar suka gina hanyar tare. Tun daga fara gina hanyar, an riƙa fuskantar ƙalubaloli da cutar COVID-19 ta haifar, kuma kamfanonin sun yi aiki kafaɗa da kafaɗa don kandagarkin cutar, da kuma gudanar da aikin. A waje ɗaya kuma, kamfanin Sin ya dora muhimmanci kan horar da matasan ma’aikata na Masar fasaha, domin samar da taimakon kwarewaga tawagar masu ginawa da kulawa da layin dogon.

Mai fassara: Safiya Ma