An bankaɗo ɓoyayyiyar shinkafar tallafi da Gwamnatin Tarayya ta aika Kano

Daga USMAN KAROFI

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta kai sumame a wata ma’ajiya da ke unguwar Hotoro Ring Road, kusa da Farin Masallaci, inda aka gano ana sauya buhunan shinkafa 16,800 da ake zargin tallafin gwamnatin tarayya ne. Wannan shinkafa an ware ta ne don tallafawa jama’a, kuma an gano ana canza buhunta domin sayarwa a kasuwa. Shinkafar na ɗauke da hoton Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da rubutun “Ba don sayarwa ba.”

Shugaban PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado, yayin da yake jawabi a wurin sumamen, ya bayyana cewa, “Mun gano cewa wasu mutane na amfani da damammakin tallafin gwamnati don cin gajiyar kansu. Sun fara sauya wannan shinkafa da aka ware don tallafawa jama’a, don su sayar da ita a kasuwa. Wannan babban nau’in cin hanci ne, kuma a wannan mawuyacin hali da muke ciki a ƙasa, babu dalilin da zai sa wani ya aikata haka.”

Shugaban ya ƙara da cewa za a gudanar da cikakken bincike domin gano dukkan waɗanda ke da hannu a wannan al’amari. Ya bayyana cewa an kama mutum guda a halin yanzu, amma hukumar za ta yi duk mai yiwuwa don bankaɗo sauran waɗanda ke da hannu. “Za mu ɗauki matakan doka domin dakatar da irin wannan mummunan aiki da ke barazana ga tallafin da ake shirin bai wa talakawa,” inji shi.

A cewar hukumar, buhunan shinkafa da aka gano sun kai nauyin motoci 28, inda kowanne babban mota ya ƙunshi buhu 600. Shugaban ya bayyana cewa, idan aka lissafa farashin kowanne buhu a kan N82,000, jimillar kudin ya kai sama da naira biliyan 1.3. Wannan ya nuna irin asarar da za a yi wa tallafin gwamnati idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba.