An bankaɗo zargin tsohuwar almundahanar alƙalin da ya bada belin Alhassan Doguwa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An bankaɗo zagin tsohuwar almundahar kuɗaɗe da Mai Shari’a Yunusa Mohammed, wanda ya bada belin Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilan Nijeriya, Alhassan Ado Doguwa, wanda ake tuhuma da laifin kisan kai kwana guda da yin zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya na ranar 25 ga Fabrairu, 2023.

Jaafar Jaafar, Mawallafin jaridar Daily Nigerian, shi ne ya bankaɗo zargin cin hanci da rashawar sa’o’i kaɗan da sanarwar bada belin Alhassan Ado Doguwan.

A cikin bayaninsa, Jaafar ya ce NJC ta taɓa dakatar da Mai Shari’a Yunusa Muhammed biyo bayan zargin cin hanci da rashawa da rashin ɗa’a a shari’ar da ta shafi RIckey Tarfa SAN, inda aka tura kuɗi Naira miliyan 1.5 zuwa asusun ajiyarsa na banki saboda wasu dalilai da ba za a iya bayyanasu ba.

“Bayan wata ƙara mai kwanan wata 21 ga Disamba, 2015 wata ƙungiyar farar hula mai suna Civil Society Network Against Corruption, CSNAC, mai lamba NJC/F.3.FHC49/1/421, an gayyaci Yunusa da ya gurfana a Kotun Ƙoli domin amsa tuhumar da ake yi masa tare da duk takardunsa na kare tuhumar.”

Ya ƙara da cewa: “A ranar 15 ga Yuli, 2016, NJC ta ba shi shawarar yin ritaya a taƙaice, bisa shawarar kwamitin bincike.

“An same shi da laifin duk zarge-zargen da ake tuhumarsa a cikin ƙarar da CSNAC ta shigar.

“Wani abin mamaki, sai ga shi an mayar da shi kan benci bayan shekaru biyar (Janairu 2021),” inji Jaafar.