An buƙaci daraktoci su ɗauki aikinsu da muhimmanci a Kano

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye mni, ya yi kira ga daraktocin sashen wayar da kai na ma’aikatun gwamnati da hukumomi a jihar da su zama masu himma matuƙa wajen aiwatar da ayyukan da suka rataya a kansu.

Halilu ya yi wannan kira ne yayin taron fahimtar juna da tsakaninsa da daraktoci da kuma hukumomin da lamarin ya shafa.

Ya ce dalilin taron shi ne, don saka wa jami’an ƙaimi da kuma yaba musu dangane da irin ƙwazon da suke yi wajen aiwatar da harkokin gwamnati a ma’aikatunsu mabambanta.

Ya ƙara da cewa, Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf tana ƙoƙarin fitar da tsare-tsare domin horar da ‘yan jarida a jihar don ƙarfafa musu gwiwa.

Kazalika, ya ce gwamnatin jihar ta ba da himma wajen inganta rayuwar ma’aikata a jihar.

Tun da fari, Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar, Inuwa Idris Yakasai, ya ce taron na cikin gida ne kuma fage na bai wa waɗanda lamarin ya shafa damar bayyana ra’ayoyinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *