An buƙaci mazauna yankin Mabushi su bai wa hukumar VIO haɗin kai

Hakimin Mabushi da ke yankin Abuja, Alhassan Mabushi, ya ziyarci Ma’aikatar Kula da Harkokin Hanyan da Ababen Hawa, wato FCT Directorate of Road Traffic Services.

Yayin ziyarar tasa, Basaraken ya yaba wa Shugaban ma’aikatar, Dr AbdulLateef Bello dangane da shigar da shirin karɓar lambar motoci da inshora a intanet don kawar da wahalar da jama’a kan fuskanta wajen karɓar lamba.

Hakimin ya yi amfani da wannan dama wajen kira ha al’ummarsa na yankin Mabushi da su bai wa ma’aikatar cikakken goyon game da ayyukanta.

Tawagar da ta yi wa Hakimini rakiya ta ƙunshi tsohon Kodinetan Cibiyar Bunƙasa Garuruwan Gefen Abuja, Malam Tanko da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *