An buƙaci Tinubu ya tsige shugabannin tsaro biyo bayan harin bom a Kaduna

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi kira da a tsige manyan shugabannin sojoji kan harin bom da sojoji suka kai bisa kuskure a Tudun Biri, Jihar Kaduna, wanda hakan ya salwantar da rayuka sama da 85 tare da jikkata wasu da dama.

Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum kuma mamba a ƙungiyar NEF, Farfesa Usman Yusuf, shi ne ya yi wannan kira yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Channels Television a ranar Talata.

Yusuf said, “Wannan rashin dacewa ne. Dukkansu za yi murabus, a kori duk wani jami’in da ke daga cikin masu bada umarni.”

“Babban Hafsan Tsaro (CDS), kowannensu zai tafi, kuma Shugaban Ƙasa zai katse tafiyarsa ya dawo gida,” in ji Yusuf.

Ya ƙara da cewa kamata ya yi baki ɗaya shugabanni tsaro su miƙa takardar ajiye aiki saboda abin da ya faru wanda ya jefa ilahirin ƙasa cikin alhini.

Ya ce sojojin da ya kamata su kare rayukan ‘yan ƙasa su ne kuma suka ɓige da kashe ‘yan ƙasa.

Farfesan ya ce, “Baki ɗayansu (Jami’an) su tafi, CDS da CAS da GOC da shugabannin gudanarwa duk su tafi.”

A ranar Lahadin da ta gabata sojoji suka jefa bom har sau biyu bisa kuskure kan mutanen da suke taron maulidi a ƙaiyen Tudun Biri cikin Ƙaramar Hukumar Igabi a jihar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 100 tare da jikkata da daman gaske.