An buɗe kasuwar Gwandu bayan shekaru 27 da gina ta

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Ranar Juma’ar da ta gabata ne aka buɗe kasuwar garin Gwandu bayan shekaru ashirin da bakwai da gininta.

Wakilinmu ya yi tattaki zuwa garin na Gwandu inda ya zanta da Malam Abubakar Zaki daga cikin jagororin gudanarwa na ‘yan kasuwar ƙaramar hukumar mulki ta Gwandu, ya bayyana cewa an daɗe da gina wannan kasuwar amma sai dai aka bar ta nan ba a dawo ba kimanin shekaru ashirin da bakwai Allah ya kawo lokacin da za ta soma ci.

Ya yaba wa Alhaji Muhammadu Mode bisa ga irin ƙoƙarin sa na ganin an baro cikin gari inda ake gudanar da kasuwanci a halin takura saboda rashin wadataccen fili aka dawo inda kowa ya saki jiki.

Waɗansu daga cikin jagororin da wakilinmu ya zanta da su da suka haɗa da Malam Muhammadu Gwandu da Malam Muhammadu Bello sun yi addu’ar Allah ya saka wa Alhaji Muhammadu Mode da alheri bisa ga irin wannan ƙoƙarin da kuma kishin gida da ya nuna da kuma fatar Allah ya albarkaci wannan kasuwar da sauran kasuwanni.

Sakataren ƙaramar hukumar mulki ta Gwandu Alhaji Muhammadu Mode bayan ƙaddamar da kasuwar ya zanta da wakilinmu, inda ya bayyana cewa daga cikin dalilan buɗe wannan kasuwar shi ne, a matsayin sa na mai kishin yankin sa ko da yaushe tunaninsa bai wuce wane abu ne zai assasa na ƙwarai da zai bar tarihi ba.

Akwai samun ƙarin kuɗin shiga ga ƙaramar hukumar mulki ta Gwandu duk da ya ke ba a soma karɓar kuɗin shiga hannun kowa ba sai dai shaguna kawai da aka bai wa duk wanda ke da bukata kafin nan gaba duk da ya ke karamar hukumar mulki ta yi tanadin wadataccen ruwa ta hanyar gina bohol tare da kafa famfuna da kuma  makewayi, haka-zalika yanzu haka ana nan ana gyara hanyar shigar manyan motoci don ɗauka da sauke dabbobi a kara.

Alhaji Muhammadu Mode ya ƙara da cewa yanzu haka dai ana duba yiyuwar cin kasuwar sau biyu a mako, inda bayan ta ci rana Juma’a ta sake ci ranar Talata saboda ranar Juma’ar tana cin karo da manyan kasuwanni da suka haɗa da Argungu, Birnin Kebbi, Jega Bunza da kuma Gummi saboda akwai fatake da ke ɗaukar kayan marmari da dabbobi zuwa sassa daban-daban na kudancin ƙasar nan.