An buɗe rumbun adana wallafe-wallafe da al’adun gargajiya na Ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA

An ƙaddamar da ginin rumbun adana wallafe-wallafe da al’adun gargajiya na ƙasar Sin a jiya a Asabar.

Ginin wata muhimmiyar alama ce ta al’adun gargajiya a sabon zamani, haka kuma cibiyar adana al’adun gargajiya ta ƙasar Sin.

Bayan buɗewar, zai gudanar da ayyukan wallafa da adana muhimman kayayyaki da al’adun gargajiya da aka yi gado.

Babban ɗaki mai lamba 1 na ginin, ya ƙaddamar da jerin nune-nune na musammam bisa taken raya tarihin Sinawa da ci gaban wayewarsu. Haka kuma yana haska sauye-sauyen tarihi da shaida nasarorin da aka cimma.

Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa