An buƙaci a dawo da aikin duba-gari a Jihar Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Kimanin sati shida kenan Hukumar Tsaftace Muhalli ta Jihar Jigawa (JISEPA) ta yi tana yashe magudanan ruwa a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, a ƙoƙarin hukumar na kare muhalli da hana afkuwar ambaliyar ruwa a lokacin ruwan damina.

Babban Manajan-darakta na hukumar,  injiniya Lawan Ahmed ya tabbatar da haka ga manema labarai a ranar Labar da ta gabata a ofishinsa.

Ya ce  ma’aikatan hukumar sun share sati huɗu a Ƙaramar Hukumar Babura suna gyaran magudanun ruwa kuma suka gudanar da feshen maganin sauro da nufin inganta rayuwar al’umma ta ɓangaren tsaftar muhalli.

Alhaji Lawan ya ƙara da cewar yanzu haka ma ma’aikatansu suna Gumel domin cigaba da bunƙasa ayyukan gyaran garin Gumel. 

Ya kuma koka akan ƙarancin ma’aikata da suke fuskanta don haka ne ma ya buƙaci gwamnatin jihar da ta ba su dama wajen qara ɗaukar ma’aikata ko da na wucin gadi ne.

Ya ci gaba da cewar ba su da wata matsala da take damunsu da ta wuce ta ƙarancin ma’aikata da kayan aiki, inda ya ce saboda ƙarancin ma’aikatan ne da ƙarancin kayan aiki masu nagarta ya sa suke fuskantar matsalolin ambaliya a lokacin damina.

Ya nuna damuwarsa matuƙa musamman a ɓangaren motocin kwashe shara da kuma motocin da suke yi wa tifofin lodin sharar kasancewar mafi yawan motocin ba su da cikakkiyar lafiya da za su gudanar da aikinsu hankali kwance.