An buɗe taron ministocin kuɗi da gwamnonin manyan bankunan ƙasashe mambobin BRICS karo na fatko a shekarar 2022

Daga CMG HAUSA

An gudanar da taron farko a bana, na ministocin kuɗi da gwamnonin manyan bankunan ƙasashe mambobin ƙungiyar BRICS ta kafar bidiyo, a jiya Jumma’a . Taron mai taken “Raya dangantakar abota mai inganci don ƙirƙirar sabon zamanin ci gaban duniya”, ya tattauna kan batutuwan da suka shafi yanayin tattalin arziki da daidaita manufofi, da sabon bankin raya ƙasa, da zuba jari kan ababen more rayuwa, da cibiyoyin binciken masana a fannin kuɗi na BRICS da dai sauransu.

Kana an yi musayar ra’ayi kan sakamakon da ake sa ran samu daga haɗin gwiwar hada-hadar kuɗi tsakanin ƙasashen BRICS a bana.

Ministan kuɗi na ƙasar Sin, Liu Kun ya bayyanawa taron cewa, a shekarar 2022, ƙasar Sin za ta ci gaba da hada hannu da ɓangarori daban daban don inganta haɗin gwiwar hada-hadar kuɗi ta ƙasashen BRICS, tare da cimma daidaito, yana mai cewa hakan zai share fage sosai kan taron ƙoli karo na 14 na BRICS a fannonin manufar kuɗi da sakamakon da za a samu.

Liu Kun ya ƙara da cewa, a halin yanzu, ƙarfin ingantuwar tattalin arzikin duniya na raguwa, yanayin ƙasa da ƙasa kuma na da sarkakiya da tsanani, kuma ci gaban duniya ya gamu da cikas. Don haka, ya kamata ƙasashen BRICS su sauke nauyin dake wuyansu, da haɗa gwiwa, da karfafa daidaituwar manufofi bisa manyan tsare-tsare, da taimakawa farfadowar tattalin arziki mai ɗorewa, da nufin samun ci gaban duniya mai karfi, da kiyaye muhalli yadda ya kamata, da kuma gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga ɗaukacin bil-Adam.

Mai fassara: Bilkisu