An caccaki Ƙatar kan cin zarafin baƙi gabanin gasar Kofin Duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu ƙasashe da babbar tawagar ƙwallon ƙafar Australiya sun caccaki jerin cin zarafin bil adama a Ƙatar, gabanin Gasar Kofin duniya da ke tafe a watan Nuwamban wannan shekarar, lamarin da ya sa Australiya kasance tawaga ta farko da ke cikin wannan gasa da ta caccaki ƙasar da ke karɓar baƙuncin gasar.

Gasar Kofin Duniya da za a fara a ranar 20 ga watan Nuwamba ta fuskanci cece-kuce tun daga lokacin da aka bai wa Ƙatar damar karɓar baƙuncin shekaru 12 da suka wuce.

Hukumar ƙwallon ƙafar Australia ta ce ta san cewa an yi sauye-sauye ga dokokin Ƙatar ta yadda za su kare haƙƙoƙin ma’aikata, kuma ta ƙarfafawa masu ruwa da tsaki gwiwa su goyi bayan sauye-sauyen.

’Yan wasan tawagar ta Australia sun ce sun samu labarin irin wahalhalun da ma’aikata baƙin haure da iyalansu ke sha a Ƙatar.

Tun da farko a wannan mako, hukumomin Ƙatar suka caccaki abin da suka bayyana a matsayin munafurci daga wasu ƙasashen duniya a game da batun take haƙƙin ɗan adam a ƙasar gabanin gasar kofin duniya ta 2022.