An cafke ɗan shekara 14 mai garkuwa da yin fyaɗe a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jami’an hukumar tsaro na Civil Defence sun yi nasarar cafke wani yaro mai suna Sani Suleiman ɗan kimanin shekara 14 da ake zargi da laifin sata da yin garkuwa da mutane a Jihar Zamfara. 

Labarin hakan ya fito ne daga bakin babban kwamandan rundar jami’an tsaron farin kaya ta jihar, A.A Spark a lokacin da yake gabatar da mai laifin ga manema labarai ranar Laraba.

 A cewarsa, an cafke Suleiman ne a ƙauyen Kadage da ke yankin Masarautar Moriki a Ƙaramar Hukumar Zurmi

 Kamar yadda rahoton ya nuna, ƙaramin yaron ya samu horo ne a dabar wani mai suna salihu da ke dajin Sububu

 Ya bayyana cewa yaron ya ƙware wajen satar shanu da kuma ayyukan garkuwa da mutane 

“Salihu ya ce shi yaron gogarman ɗan bindigar nan ne da ya yi ƙaurin suna, wato Bello Turji, da ya addabi ilahirin Arewa maso Yamma,” inji Spark.

A cewar sa, yaron ya ƙware sosai wajen yin lalata da matan da suke yin garkuwa da su a dabar tasu.

Ya ce yanzu haka suna ci gaba da gudanar da bincike, inda da zarar sun kammala za su miƙa shi kotu don yanke masa hukunci.

Jihar Zamfara, Katsina da Sakkwato dai suna fuskantar barazanar ‘yan bindigar daji da yin garkuwa da mutane, inda gwamnatin jihohin suka ɗauki matakai daban-daban don magance matsalolin, amma har yanzu ‘yan bindigar suna ƙaddamar da hare-hare a yankunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *