An cafke ɗan ta’addan da ya kashe sama da mutum 15 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina ta yi nasarar kama wani ƙasurgumin ɗan ta’adda mai suna Sulaiman Iliyasu, wanda ake wa laƙabi da ‘Yar Bishiya.

Kakakin Rundunar, Sp Gambo Isa ne ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da mai laifin ga manema labarai a hedikwatar rundunar dake birnin Katsina

SP Isah ya ce, an kama wanda ake zargin ne da laifuka daban-daban da suka haɗa da ta’addanci a faɗin jihar

Ya ƙara da cewa, wanda ake zargin ɗan shekara kimanin 28, ya shahara wajen aikata ta’addanci.

“Yana ƙarƙashin ƙungiyar ƙasurgumin ɗan ta’adda wanda hukumar ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo, wato Ɗan Ƙarami.

“Ɗan ta’addan wanda ya shahara wajen satar mutane don neman kuɗin fansa ya addabi al’ummar yankunan Jibia, Ɗaɗɗara, Sabuwa, Faskari, Kurfi, Ɗandume da ma yankin Ɗanmusa.”

Da yake magana gaban manema labarai, wanda ake zargin ya ce ya kashe mutane sama da 15 tun da ya shiga aikin ta’addanci.