An cafke dillalin ƙwayar da ke da alaƙa da badaƙalar Abba Kyari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

NDLEA ta cafke Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, ƙasurgumin dillalin ƙwayoyi, wanda shi ne ummul-aba-isi na cinikin ƙwayar Tramadol ta Naira biliyan 3, wacce a ke tuhumar dakataccen ɗan sandan nan, Abba Kyari. 

Ukatu, wanda shine Shugaban Rukunin Kamfanin Mallison, dubun sa ta cika ne bayan watanni a na fakon sa kuma ana ta kulli-kurciya da shi.

An dai cafke shi ne a cikin jirgin sama a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas a kan hanyarsa ta zuwa Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Afrilu.

Binciken hukumar NDLEA ya bayyana cewa shi ne babban dillalin shigo da ƙwayar Tramadol mai nau’i daban-daban da su ka haɗa da mai ƙarfin giram 120, 200, 225 da 250 cikin ƙasar nan.

Ukatu na da kamfanin magunguna da na robobi, in da ya ke amfani da su wajen yin basaja domin ya shigo da miyagun ƙwayoyi cikin ƙasar nan, inda kuma a ka gano ya na da asusun banki har 103 da ya ke amfani da su wajen badaƙalar kuɗaɗe.

An fara sanya ido a kan Ukatu ne a bara bayan da a ka kama wani ma’aikacin sa da katan 5 na Tramadol mai nauyin giram 225 a ranar 24 ga watan Mayu, 2021 lokacin da ya tafi ya sayar wa da wani ɗan sanda da ya ke cikin tawagar Abba Kyari kuma ya yi basaja a matsayin mai sayen ƙwayoyi a Ikeja ta Jihar Legas.

A tuna cewa Kyari tare da wasu mutane huɗu na tawogar sa na fuskantar shari’a a Babbar Kotun Tarayya a Abuja a kan irin wannan laifin.