An cafke malami kan yi wa ɗalibansa 4 fyaɗe a Gombe

Daga BASHIR ISAH

‘Yan sanda a Jihar Gombe sun cafke wani malamin makarantar Islamiyya bisa zargin yi wa ɗalibansa huɗu fiyaɗe.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya rawaito cewar yaran da lamarin ya shafa ‘yan shekara tsakanin takwas zuwa 14 ne, kuma dukkansu ‘yan gida ɗaya ne.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Gombe, ASP Mahid Abubakar, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar manema labarai da ya fitar.

Ya ce a ranar 7 ga Maris aka kama wanda ake zargin bayan shigar da rahoto da mahaifin yaran ya yi kan abin da ya auku ga ‘ya’yan nasa tsakanin Janairu da Maris.

Bayanan ‘yan sanda sun nuna wanda ake zargin ya aikata laifin ne a wata makarantar Islamiyya da ke yankin rukunin gidaje na Malam-inna a Gombe.

“An kwashi yaran zuwa asibiti domin duba lafiyarsu,” in ji jami’in.

Abubakar ya ƙara da cewa, wanda ake zargin ya yi iƙirarin aikata laifin kuma za a gurfanar da shi a kotu ba da daɗewa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *