An cafke malamin addini da ƙoƙon kan mutum

Daga WAKILINMU

Wani wanda ya kira kansa malamin addinin Musulunci mai shekaru 55, Tunde Olayiwola, ya amsa cewa ya sayo sabon ƙoƙon kan ɗan’adama a Ajabbale, Oka a jihar Ondo.

Olayiwola, wanda ’yan sanda na jihar Ondo suka yi holensa ya ce, ya sayo kan bil adaman ne domin a yi masa asirin kuɗi.

A hirar da ka yi da shi, wanda ake zargin da ya bayyana cewa, shi ɗan asalin garin Osogbo ne a jihar Osun, ya ce, ya siya ƙoƙon ne kan kuɗi Naira 60,000 domin a masa asiri.

Ya ce, “wani mutum da muka haɗu a wurin taro ne ya kawo min kan har gida na a safiyar ranar Alhamis. Ina ƙoƙarin fara yin asirin ne a yayin da jami’an ’yan sanda suka yi ram da ni. Na buƙaci a kawo min kan ɗan adam ne domin in kyautata rayuwata kuma aka kawo min. Wannan shi ne karo na farko, amma ina son in yi arziki ne domin in yi rayuwa mai daɗi. A yau aka kawo min ƙoƙon kan.”

Da ya ke magana kan lamarin, kwamishinan ’yan sandan jihar Ondo, Oyeyemi Oyediran, ya ce, “jami’an ’yan sanda sun kama wanda ake zargin ne sakamakon bayanan sirri da suka nuna cewa yana daf da karɓar wani saƙo.”

Oyediran ya ƙara da cewa, “an kama wanda ake zargin a lokacin da aka kawo masa sabon ƙoƙon kan kuma ya amsa cewa yana da niyyar yin asiri da kan ne domin ya inganta rayuwarsa.”

Ya ce, “a ranar 23 ga watan Disamban 2021, misalin ƙarfe 9 na safe, ’yan sanda sun samu bayani cewa wani da ke kiran kansa malami mai suna Alfa Tunde Olayiwola, wani da ake zargin mai tsafi ne yana daf da karɓar saƙo da ake zargin kan ɗan’adam ne.”

A wani labarin mai alaƙa da wannan, rundunar ’yan sandan jihar Ogun ta kama wani ɗan shekara 55, Yesiru Salisu da laifin mallakar sassan ɗan’adam da suka haxa da ƙoƙon kai guda huɗu, busassun hannaye biyu da muƙa-muƙi guda uku.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyayemi ya fitar, kama wanda ake zargin ya biyo bayan wani rahoto da aka shigar a ofishin ’yan sanda na Ago Iwoye.

Mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa, rahotannin sun bayyana cewa an ga wanda ake zargin da jakar da ake zargin kayan sata ne, kuma da aka tambaye shi meye a jakar, sai ya yar da jakar ya gudu daji.