An cafke masu ƙoƙarin kitsa juyin mulki a Sierra Leone

Daga BASHIR ISAH

‘Yan sanda a ƙasar Sierra Leonean sun ce sun tsare mutane da dama, ciki har da jami’an soji waɗanda ke shirin kai harin tada zaune tsaye a ƙasar.

Wannan na zuwa ne shekara guda bayan mummunan rikicin da ya auku a ƙasar a watan Agustan 2022, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 30.

‘Yan sandan sun ce “Ɓangaren tsaron ƙasar na bibiyar bayanan sirri dangane da ayyukan wasu ɗaiɗaikun ‘yan ƙasar, ciki har da sojoji waɗanda suke ƙoƙarin daburta zaman lafiya a ƙasar.

Jami’an sun ƙara da cewa, waɗanda ake zargin sun shirya yin amfani da damar zanga-zangar lumanar da ake shirin gudanarwa ya zuwa makon gobe don kai farmaki a wurare daban-daban.

Hauhawar farashin kayayyakin masarufi da nuna halin ko-in-kula daga ɓangaren gwamnati ne suka haifar da rikicin da ya laƙume rayuka da dama a Agustan 2022.