An cafke masu ƙwacen waya da ƙauraye 74 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Katsina, ta kama wasu masu aikata miyagun laifuka a jihar da suka haɗa da masu ƙwacen waya da ƙauraye da masu safarar miyagun ƙwayoyi da mata masu zaman kansu da kuma masu ba wa ‘yan ta’adda bayanan sirri da yawan su ya kai 74.

Kakakin rundunar, CSP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a Hedikwatar rundunar da ke Katsina babban birnin jihar, a lokacin da yake gabatar da su ga manema labarai.

Kakakin rundunar ya bayyana cewar, an kama waɗanda ake zargin ne bayan wani samame da rundunar ta kai, inda aka kama mutane da suka haɗa da maza 70 da mata huɗu a unguwanni daban-daban dake babban birnin jihar.

Idan zaa iya tunawa, Manhaja ta rawaito labarin umarnin da Kwamishinan ‘yan sanda mai riƙon ƙwarya a jihar, ya bayar inda ya umarci jami’an rundunar a kan su tabbatar sun cafko masu ƙwacen wayoyin jama’a da kuma ƙauraye da suka addabi jihar.