An cafke matashin da ke lalata da ƙaramin yaro a Jigawa

Daga UMAR  AKILU MAJERI a Dutse

Dubun wani matashi mai  kimanin shekaru talatin a duniya ta cika adaidai lokacin da malaman makaranta suka gano ɗaya daga cikin ɗaliban su yana wadaƙa da kuɗi, inda bincike ya yi zurfi aka samu labarin wannan matashi mai suna Abdullahi, mazaunin unguwar Maranjuwa da ke lalata da shi a gidansa idan matarsa ba ta nan.

Lamarin da ya sa hukumar makarantar ta samar da iyayen yaron halin da ɗansu yake ciki, kuma suka sanar da jami’an Civil Defense aka cafke wanda ake tuhumar, yayin da bai musa ba ya tabbatar da abinda ake tuhumarsa a gaban jami ‘an tsaron bayan da likitoci suka bada bayanan shaidar cewar hakan ta faru tsakanin yaron da kuma matashin da ake tuhuma.

 Yaron mai kimanin shekaru sha ɗaya a duniya ya ce ba sau uku ne aka yi masa luwaɗin ba kamar yadda ake tuhumar, ya faɗa wa jami’an tsaro cewar shi kansa bai san adadin yadda ya yi luwaɗin da shi ba; ya yi a gidansa idan matarsa ba ta nan ta je unguwa, kuma ya yi da shi a cikin kangaye a cikin unguwa. Idan ya gama kuma ya ba shi kuɗi da biskit, wani lokacin kuma ya ba shi kuɗi da alawar milk candy har ma da agogon hannu.

Yanzu haka dai wanda ake tuhumar yana hannun jami’an tsaro yana amsa tambayoyi, kuma da zarar sun kammala bincike a kansa za su gurfanar da shi a gaban alƙali domin ya sari abinda ya shuka, saboda hakan ya zama darasi ga masu irin halinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *