An canja jadawalin fara gasar kofin duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Za a fara gasar kofin duniya ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba, inda Ƙatar mai masaukin baƙi za ta kara da Ecuador.

Tun farko an tsara karawar rukunin farko ranar 21 da ƙarfe 16:00 agogon GMT, kuma wasan Ƙatar shi ne na uku daga cikin wanda aka tsara yi.

An shirya da buɗe gasar da wasa tsakanin Senegal da Netherlands ranar Litinin 22 ga watan Nuwamban.

Daga baya FIFA ta karɓi ƙorafi daga hukumar ƙwallon ƙafa ta Kudancin Amurka da ake kira Conmebol, wadda ta ce bisa al’ada ana bikin buɗe gasa ko dai da mai riƙe da kofi ko kuma mai masaukin baƙi.

Za a zauna taro tsakanin hukumomin nahiyoyin duniya shida da shugaban FIFA, Gianni Infantino don fitar da matsaya.

Idan aka amince ba za a sauya ranar karawa tsakanin Senegal da Netherland ranar Litinin ba, illa wasan zai koma da ƙarfe 16:00 agogon GMT.

Abinda zai sauya a ranar Litinin shi ne fafatawa uku za a yi maimakon huɗun da aka tsara tun farko.

Za a buga wasan da aka shirya yi a rukuni na biyu tsakanin Ingila da Iran da qarfe 13:00 GMT ranar 21 ga watan Nuwamba da kuma na Wales da Amurka da ƙarfe 21:00 agogon GMT.