
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Laraba ne jami’an tsaro a ƙasar Pakistan suka yi nasarar ceto wasu fasinjoji guda 155 daga wani jirgin ƙasa da aka ƙwace a yankin Kudu maso yammacin Balochistan.
Jirgin, wanda ke ɗauke da kimanin mutane 450 ciki har da jami’an sojoji da iyalansu, ya samu farmaka ne daga wasu ƴan bindiga sama guda 100 daga cikin ƴan tawayen Baloch Liberation Army (BLA), ranar Talata.
A lokacin da sojoji suka kai ɗauki a wajen da lamarin ya faru, sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda guda 27, kamar yadda wata majiya ta tsaro ta bayyana.
Mayaƙan ƴan tawayen suna amfani da fasinjojin ne wajen kare kawunansu daga hare-hare da kuma aika wasu ƴan ƙunar baƙin wake ɗauke da rigunan ababen fashewa zuwa inda waɗanda aka kama suke.
Rahotanni daga gidajen jaridun ƙasar sun ce aƙalla mutane 10 ne har da direban jirgin suka rasa rayukansu a yayin ba-takashi tsakanin jami’an tsaro da mayaƙan.
Zuwa lokacin kammala rahoton, ba a san adadin waɗanda suka samu raunuka ba daga bangarorin sojoji da fasinjoji da mayaƙan ba, bayan ɗaukar tsawon
sa’o’i ana fafatawa.
Ƴan tawayen BLA, waɗanda a baya sun yi ta kai farmaki ga jiragen ƙasa da motoci da ke ɗauke da jami’an sojoji, sun ɗauki alhakin kai harin tare da neman a yi musayar fursunonin a tsakanin su gami da barazanar kashe waɗanda ke hannunsu matuƙar aka cigaba da kai masu hari.