An ci tarar Firaministan Birtaniya saboda rashin ɗaura bel a mota

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An ci tarar Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak saboda rashin sanya bel a mota yayin da ya ke ɗaukar hoton bidiyo na dandalin sada zumunta.

‘Yan Sandan Lancashire sun ce sun bayar da wannan umurni ne daga Landan tare da yanke hukunci.

Wani mai magana da yawun Downing a ranar Juma’a ya ce, Mista Sunak ya amince da wannan kuskure ne kuma ya nemi afuwa, ya ƙara da cewa zai biya tarar.

Fasinjojin da aka kama ba tare da sanya bel ɗin kujera ba ana iya cin tararsu fam 100.

Wannan na iya ƙaruwa zuwa Yuro 500 idan shari’ar ta kai kotu.

Firayim Ministan ya kasance a Lancashire lokacin da yake ɗaukar hoton bidiyon, yayin wata tafiya a arewacin Ingila.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Mista Sunak ke samun sanarwar hukunci yayin da yake gwamnati.

A watan Afrilun da ya gabata, an ci tarar shi tare da Boris Johnson da matarsa Carrie saboda karya ƙa’idojin kullen Korona ta hanyar halartar taron ranar haihuwar firaminista a Titin Downing a watan Yuni 2020.