An ci tarar GT Bank da bankuna huɗu kan haramtacciyar harƙallar kuɗi

Daga AMINA YUSUF ALI

Babban Bankin Nijeriya (CBN) da kuma hukumar kula da hada-hadar hannun jari ta ƙasa (SEC) sun ci tarar wasu bankuna guda biyar a kan laifuffuka har guda ashirin da suke da alaƙa da haramtacciyar harƙallar kuɗi da kuma karya dokar canjin kuɗi, inda aka caji kamfanonin jimillar tarar Naira biliyan guda da kusan rabi. 

Bankunan da abin ya shafa su ne: Guaranty Trust Holding Company Plc, United Bank for Africa Plc, Access Bank Plc, Stanbic IBTC Holdings Plc da kuma Fidelity Bank Plc.

Daga cikin bankunan, Bankin GT Holding shi ya fi amsar tara ma fi yawa, inda zai biya fiye da rabin ku]in tarar. Wato dai gwari-gwari fiye da rabin Naira biliyan wato Naira miliyan  N692.

Sai kuma bankin UBA da yake dafe masa baya, aka ci shi tarar Naira miliyan N273. Sai kuma bankin Stanbic da ka ci shi miliyan 233. Sannan kuma bankin Access, Naira miliyan, N189. Sai kuma bankin Fidelity da aka ci shi tarar Naira miliyan N65.15.