An daɓa wa jarumi Saif Ali Khan wuƙa sau shida a gidansa

Kamar yadda BBC Hausa ya ruwaito a jiya Alhamis ne aka yi wa fitaccen jarumin finafinan Bollywood, Saif Ali Khan, tiyata biyo bayan daɓa masa wuƙa a lakarsa da wani mutumi ya yi bayan ya kutsa cikin gidan jarumin, kamar yadda masu taimaka ma sa su ka ce.

Harin dai ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar da jarumin da iyalansa ke zaune a wajen birnin Mumbai.

’Yan sanda sun shaida wa BBC cewa, an dai kai wa jarumin harin ne sakamakon wata hatsaniya da ta ɓarke tsakaninsa da wani mutum da ba a san kowane ne ba wanda ya kutsa har cikin gidan jarumin da tsakiyar dare.

Zuwa yanzu ba a samu cikkaken bayani kan harin ba.

”Daga nan sai gardama ta ɓarke tsakanin Khan da maharin, ” kamar yadda mataimakin kwamishinan ƴan sandan Mumbai Diɗit Gedam ya shaida wa BBC.

An garzaya da Khan asibitin Lilaɓati da ke birnin Mumbai da safiyar Alhamis.

Niraj Uttamani, wani babban jami’i a asibitin ya shaida wa BBC cewa an daɓawa khan wuƙa sau shida, amma biyu ciki sun fi muni.

” Mu na buƙatar ƴan jarida da magoya bayansa su yi haƙuri su kwantar da hankalinsu. Lamarin ya na hannun ƴan sanda,” a cewar masu kula da jarumin.

Ƴansandan dai sun haɗa wata tawagar da za ta binciki al’amarin.

“An yi wa Khan tiyata kuma ya fito lafiya. Yanzu haka yana murmurewa kuma likitoci na sa ido kansa,” a cewar masu taimakawa Khan cikin wata sanarwa.

Da yake magana da manema labarai bayan tiyatar, Dakta Nitin Dange na asibitin Lilaɓati inda aka kwantar da Khan, ya ce jarumin ya samu mummunan rauni a laƙarsa sakamakon daɓa masa wuƙa a lakar.

Saif Ali Khan na auren fitacciyar jaruma Kareena Kapoor, inda suke da ƴaƴa biyu.

Zuwa yanzu ba a ji ta bakin iyalinsa ba, sai dai masu taimakawa Khan sun tabbatar da cewa suna cikin ƙoshin lafiya.