An daina kishi na faɗan baki, sai na ƙwandala – Khadija Mahuta

Hajiya Khadija Abdulrasheed Mahuta mace ce wadda ya kamata mata su yi koyi da ita, kasancewar ta jaruma kuma tsayayya, sannan da ta san ciwon kan ta. Ta kasance cikin jerin mata da su ke tauna taura biyu a lokaci guda. Ma’ana, mace ce wadda ba ta zauna ba don jiran sai wani ya samo ya kawo mata, a’a, ta tashi tsaye ne haiƙan wajen rufa wa kan ta asiri. Wakiliyar Manhaja ta tattauna da ita inda ta bayyana wa masu karatu rayuwar ta wadda za ta iya zama makaranta ga mata.

Daga AISHA ASAS

Masu karatu za su so ki gabatar masu da kan ki.
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Da farko dai suna na Khadijat Abdulrasheed Mahuta. Ni haifaffiyar cikin garin Kaduna ce. Na yi karatu matakin firamare zuwa jami’a. Na tava aure da samun albarkar yara.

Mece ce sana’ar ki?
Sana’a ta ita ce noman kajin gidan gona da kifi. A gefe ɗaya kuma ina rubutun littattafan faɗakarwa na Hausa.

Mene ne matsayin sana’a ga ‘ya mace a wannan zamani?
Matsayin sana’a ga ‘ya mace a wannan zamani ba ma sai an ce ma mace “tashi ki yi sana’a ba”. In dai mace na da hankali, to za ta tashi ta nemi na kan ta. A halin da ake ciki yanzu mun kawo zamanin da ko dangin ka na da kuɗi, to dole ka miƙe ka nemi naka don kwanciyar hankalin ka da tsira da mutuncin ka. Mace na sana’a don ta rufa wa kan ta asiri; mace na sana’a don ta rufa wa mijin ta da ‘ya’yan ta da sauran dangin ta asiri.

Kin fuskanci ƙalubale ta wannan sana’ar taki?
Ƙwarai, na fuskanci ƙalubale musamman wasu lokuta sai kajin su yi ta mutuwa, a maimakon riba sai faɗuwa. Amma duk da haka ban fasa ba, na jure.

Nasarori fa?
Na samu nasarori da dama. Nasara babba da na samu ita ce ina biya wa kai na buƙatu sosai, wanda idan da a ce ba na yin sana’ar, to abubuwa sai ki ga sun cakuɗe wa mutum. Saboda haka babu abin da zan ce sai godiyar Allah.

Kin zaɓi sana’ar noman kaji da kifi, ko me ya sa ki sha’awar yin su?
E, to, na tava sana’o’i kala-kala, kamar ɗinki da saƙar kayan sanyi na jarirai. Na kuma yi sana’ar kayan shafe-shafe, wato ‘cosmetics and soaps’, wanda har ta kai ga na buɗe wajen koyar da ƙananan sana’o’i ina koya wa mata, kuma har littafi na buga musamman don sana’o’in. Amma sai na samu ƙalubale na durƙushewar kasuwanci. To da ma ina taɓa kiwon kajin kaɗan-kaɗan, sai na lura ya fi karɓa ta. Sai kawai na tsayar da komai na rungume ta.

A lokacin da ki ke koyar da mata sana’ar ta kayan ƙawa, shin gwamnati ce ke tallafawa ko kuwa matan ne ke sa aljihun su?
Na farko da na fara wata ƙungiya ce ta taimakon mata da matasa ta ɗauki nauyi. Sai kuma wata ƙungiya ana ce mata ‘U Green’ ta ɗauke ni na koya wa matan sojoji a garin Jaji da ke cikin Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna. Sai kuma wani ɗan majalisa a Jihar Katsina ya tava ɗaukar nauyi shi ma don koyar da sana’o’in. Akwai kuma wasu makarantun Islamiyyu na mata da su ka ɗauki nauyin kawunan su.

Wace kala ki ka fi so?
Na fi sha’awar ruwan ƙasa.

Wane irin kaya ki ka fi sha’awa?
Na fi sanya atamfa.

Za mu iya sanin kalar abincin da ki ka fi so?
Na fi son tuwo miyar kuka da nama.

“Namiji ba ɗan goyon ba ne”, furucin mata da yawa kenan. Amma ke meye naki furucin?
Sun kasu kashi-kashi. Akwai na goyawa har da majanyi, akwai kuma waɗanda ko saɓa su ba za a iya yi ba.

Wace shawara za ki ba mata masu zaman kashe wando?
Shawara ta gare su ita ce idan ka zauna za ka ga ana yi ba da kai ba. A wannan zamanin ko ashobe ma ya ishi mutum. Ga rayuwa yanzun ta yi tsada. Zamanin zama a yi ta ‘yan gulmace-gulmace ya ƙaura. Wallahi, ko masu kishiyoyi yanzun sun daina faɗan baki, sai na ƙwandala. In ki na da sana’a ki shiga gidan suna da biki ki na taƙama ki na hura hanci. Ko kyauta yanzun zamani ya zo da ba a yi wa wanda bai da shi.

Da yawa su na ɗora laifin talaucin su kan gwamnati, har ta kai idan ka tambaye su sana’a sai su ce gwamnati ba ta ba su tallafi ba. Shin a naki hange su na da gaskiya?
Ba su da gaskiya! Babu dalilin da mutum zai zauna ya ce zai jira gwamnati ta taimake shi. Allah ya ce tashi in taimake ka. Ni a gani na har da rashin zuciya da rashin sanin ciwon kai. Gwamnati nata ta tallafa ta buɗe hanyoyi yadda abubuwa za su zo da sauƙi. Amma ba zai yiwu ki zauna ba cas ba as ba, ki ce wai laifin gwamnati.

Kin kasance marubuciya da ta yi suna a duniyar rubutu. Shin kin kai matsayin da ki ke fatan ki kai a harkar rubutu?
Alhamdu lillah, zan iya cewa na kai matsayin da na ke son kaiwa, saboda shi rubutu, a nawa ra’ayin, na ɗauke shi ne a matsayin isar da saƙo. To kuma saƙonni na sun kai tunda ina zaune zan ga kiran waya, mace za ta fara da godiya, ka ji ta ce littafin ki ya zo daidai da matsala ta. Na gode na ji daɗi. Kuma na samu ɗaukaka da aka karanta littafi na ‘Fitila’ a gidan rediyon FRCN. Sanadiyyar haka wasu ƙungiyoyi su ka kira ni su ka ba ni ‘award’. An faɗakar da rubutu na, ɗalibai kusan uku su ka yi ‘project’ da littattafai na. To ko a haka zan iya cewa alhamdu lillah.
Kuma babu duniyar marubutan da za ka shiga yau dai ka ambaci sunan Mahuta a ce ba a san ta ba.

Harkar littafi sana’a ce ko sha’awa?
Ni dai na fara rubutu ne saboda wasu matsalolin da na ke gani su na damun al’ummar mu. To sai na fara rubutun don isar da saƙon saboda asali na ni mai sha’awar karance-karance ce. To a nan na san muhimmancin isar da saƙo ta hanyar rubutu. Shi ya sa ni ma na fara. Daga baya na fahimci cewa za a iya ɗaukar rubutu a matsayin sana’a.

Kin taɓa siyasa?
Ina taɓa siyasa, don rayuwa siyasa ce, kuma ni mutum ce mai son gwagwarmaya a rayuwa, ba na ƙaunar zama waje ɗaya.

Mu na godiya, Hajiya Mahuta.
Ni ke da godiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *