Hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya ta dakatar da ɗan ƙwallon Atletico Madrid, Angel Correa wasa biyar, saboda zagin alƙalin wasa da ya yi.
An bai wa ɗan wasan tawagar Argentina jan kati kai tsaye a minti na 88 a wasan da Getafe ta doke su 2-1 a La Liga ranar Lahadi.
Hakan ya biyo bayan ketar da Correa ya yi wa Djene, wanda VAR ta duba lamarin ta kuma tabbatar da laifin.
Daga nan ɗan wasan Atletico ya dinga zagin alƙalin wasa, Cuadra Fernandez, wanda ya rubuta rahon abin da Correa ya yi masa.
Hukuncin ya ƙunshi dakatarwar wasa ɗaya kan jan kati, sai fafatawa huɗu saboda zagin Alƙalin wasa.
Kenan Correa, mai shekara 30 ba zai buga wa Atletico wasa biyar nan gaba ba, sakamakon hukuncin.
Ba zai fuskanci Barcelona ba ranar Lahadi a La Liga da karawa da Espanyol da Sevilla da Valladolid da wasa na biyu zagayen daf da ƙarshe a Copa del Rey da Barca.
Correa ya ci ƙwallo bakwai a wasa 38 a Atletico a dukkan karawa a kakar nan.