Daga MAHDI M. MUHAMMAD
An dakatar da ɗan wasan Juventus, Paul Pogba kan zargin karya dokar shan abubuwan kara kuzari ga ‘yan wasa.
Hukumar Hana Shan Abubuwan Ƙara Kuzarin Wasa ta Italiya (NADO) ta ce, ta samu wani sinadari fiye da ƙima a jikin Pogba, bayan tashi daga karawar da Juve ta ci Udinese 3-0 ranar 20 ga watan Agusta.
Ɗan ƙwallon na tawagar Faransa, mai shekara 30 ya yi zaman benci a karawar, amma aka zaɓo shi cikin jerin ‘yan wasan da aka gwada bayan karawar.
Idan aka samu Pogba da laifi za a iya dakatar da shi shekara biyu zuwa huɗu.
Juventus ta fitar da sanarwa cewar “Rana ta ranar 11 ga watan Satumbar 2023, ta samu umarnin dakatar da Pogba daga hukumar kula da hana shan abubuwan qara kuzarin wasa, bayan samun sakamakon gwaji da aka yi masa ranar 20 ga watan Agustan 2023.
An bai wa Pogba nan da kwana uku, domin ya kare kansa kan zargin da ake yi masa.
Juventus ta sake ɗaukar Pogba kan kwantiragin kaka huɗu a Yulin 2022, bayan da ya kammala kwantiraginsa da Manchester United.
A baya dai, Paul Pogba ya ce yana duba yiwuwar yin ritaya daga taka leda, bayan ya zargi ɗan uwansa, Mathias da haxa baki da gugun ‘yan ta’adda, inda suka riƙa yi masa barazana da karɓar kuɗaɗensa.
Ɗan ƙwallon Juventus, mai shekara 30 ya shigar da ƙorafi ga masu shigar da ƙara a birnin Turin cikin watan Yulin 2022, inda ya ce an buƙaci ya biya sama da fam miliyan 11.
An tsare ɗan uwan Pogba, Mathias Pogba a watan Satumban 2022 daga baya aka sake shi a watan Disamba.
Mai shekara 33, ya musanta zargin da ake yi masa.
Da yake amsa tambayar da aka yi masa a Al Jazeera, kan yadda batun ya shafi rayuwarsa, Pogba ya ce ”Duk abin da ya haɗa da kuɗi to ka yi taka-tsantsan. Kuɗi na sauya mutane. Zai iya tarwatsa ‘yan gida ɗaya, zai iya haɗa yaƙi.
“Wani lokaci nakan yi tunani, ba na son na ƙara samun kuɗi. Kawai zan ji ba na son ci gaba da taka leda, kawai ina jin na koma mutum kamar kowa, yadda za a kaunace ni, ko ni wane ne ba don fice ko kuɗin da nake da shi.
Masu shigar da ƙara a Faransa sun fara ɗaukar mataki na shari’a a watan Satumba, wata biyu tsakani bayan Gasar cin Kofin Duniya a 2018, lokacin da Pogba ya shigar da ƙorafi.
Mai shigar da qara a birnin Paris, Laure Beccauau ta ce cikin binciken da suke yi, akwai batun cin amana da yaudara da haɗa kai da gungun ‘yan ta’adda da sace mutum don biyan kuɗin fansa da haɗa baki don aikata laifi.
Bayan tsare Mathias a watan Satumba, lauyansa Yassine Bouzrou ya ce ɗan uwan Pogba bai aikata laifin komai ba.
Pogba ya koma Juventus, bayan ƙarewar yarjejeniyarsa a Manchester United ƙarshen kakar 2022.
Mathias shi ma, qwararren ɗan ƙwallo ne, wanda ya buga wa tawagar Guinea da wasu ƙungiyoyi a Turai da suka haɗar da Crewe da Wrexham da Crawley da kuma Partick Thistle a Burtaniya.