An dakatar da rajistar masu zaɓe a Jihar Bauchi

Daga WAKILIN MU

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ɗage aikin rajistar masu zaɓe da ake yi a Jihar Bauchi.

Wannan bayanin ya ba ƙunshe ne a sanarwar da shugaban wayar da kan masu zaɓe da yaɗa labarai na INEC a jihar, Alhaji Adamu Gujungu, ya bayar a ranar Litinin a Bauchi.

Gujungu ya ce dakatar da aikin, wanda na wani taƙaitaccen lokaci ne, zai fara aiki daga ranar 21 ga Satumba, domin a samu damar kafe rajistar masu zaɓe da aka fara yi.

Ya ce ita wannan rajista da aka yi
za a kafe ta ne a hedikwatar hukumar da kuma ofisoshin INEC da ke yankunan ƙananan hukumomi 20 da ke jihar.

Ya ce, “INEC ta na so ta sanar da jama’a cewa aikin kafe rajistar domin mutane su kawo kuka ko neman gyara za a yi shi ne daga ranar Juma’a, 24 ga Satumba zuwa Alhamis, 30 ga Satumba, 2021.″

A cewar sa, aikin zai bada dama ga waɗanda su ka yi rajista su duba su tantance cewa babu kurakurai, tsallake ko ƙari a sunayen su.

Hakan, inji shi, zai ba su damar yin koke domin a gyara inda ya kamata.

Gujungu ya ce masu yin rajista za su kuma iya ganin wasu kurakuran kamar rajistar waɗanda ba ‘yan ƙasar nan ba ne, ƙananan yara ko shigar da sunayen waɗanda su ka rasu a cikin rajistar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *