An dakatar da Sheikh Nura Khalid daga limanci saboda zazzafar huɗuba

Daga WAKILINMU

Kwamitin kula da masallacin rukunin gidajen ‘yan majalisu da ke unguwar Apo a Abuja, ya dakatar da babban limamin Masallacin, wato Shiekh Nuru Khalid kan huɗubarsa ta ranar Juma’a.

Cikin huɗubarsa ta ranar Juma’ar da ta gabata, Sheikh Nura Khalid ya caccaki gwamnatin Buhari kan kasa magance matsalar tsaro da kuma yawaitar kashe-kashen rayuka a Nijeriya.

A cikin huɗubar tasa, malamin ya faɗi matakin da ya kamata talakawa su ɗauka idan har gwamnati ta bari aka ci gaba da kashe su, na ƙin fitowa zaɓe.

“Sharaɗin talakan Najeriya ya zama guda ɗaya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zaɓe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zaɓe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zaɓe,” in ji Sheikh Nura Khalid a cikin huɗubarsa.

Da alamai huɗubar ba ta yi wa kwamitin masallacin daɗi ba wanda hakan ya sanya shi ɗaukar matakin dakatar da shi daga limancin masallacin.