Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar ’Yan Sanda a jihar Kano ta ce ta kama wani ƙasurgumin ɗan daba da ake nema ruwa-a-jallo mai suna Inuwa Zakari wanda aka fi sani da Gundura.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ’yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce an kuma samu nasarar kama wasu ɓata-gari 14 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a samamen da suka yi ranakun 25 da 27 ga watan Oktoba.
Kiyawa ya ce ɗan daban ya addabi al’ummar kwaryar birnin Kano saboda irin laifuka da yake aikatawa.
“Ya kuma kasance wanda ya haɗa baki da wasu wajen kai hari kan kwamandan ’yan bijilanti har suka raunata shi ta hanyar cire masa hannu, da kuma lalata motar ’yan sanda a wani lamari na daban,” inji Kiyawa.
Kakakin ’yan sandan ya ce, a na ci gaba da gudanar da bincike kan waɗanda ake zargin a sashen binciken manyan laifuka na rundunar, inda daga bisani za a tura su zuwa kotu domin su fuskanci hukunci.
Ya ce, rundunar ba za ta lamunci ayyukan ‘yan daba ba da kuma aikata sauran laifuka a jihar.