An damƙe gurgu na sayar da ƙwaya a cikin kekensa na guragu

Wani abin mamaki ya faru yayin da wani gurgu da ke amfani da kekensa na guraru wajen ya ke sayar da miyagun ƙwayoyi a lunguna da saƙo.

Kakakin Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) na ƙasa, Femi Babafemi, ya ce an kama gurgun ɗauke da tabar wiwi mai nauyin kilo gram 1.3 da kuma lita 10 na kwayar Monkeyy Tail, a samame da hukumar ta kai matattarar masu shaye-shaye a yankin Ekpoma na Ƙaramar Hukumar Esan ta Arewa ta Jihar Edo.

Ya sanar a Abuja ranar Lahadi cewa bayan gurgun, an cafke wata matashiya mai shekaru 19 ɗauke da miyagun ƙwayoyi iri-iri da kuma kilo gram 50 na tabar wiwi a ɓoye a yankin Irrua na jihar ana shirin yin fataucinta.

Jami’an NDLEA a Jihar Edo sun kuma cafke wata mata ’yar shekara 46 da lita huɗu na ƙwayar da ake kira Wutsiyar Biri ‘Monkey Tail’ a unguwar Ugbegun da ke Ƙaramar Hukumar Esan ta Tsakiya.

“A Jihar Taraba an kama wani da kwaya 10,009 na tramadol a ranar 17 ga watan Afrilu,” in ji Babafemi.

Hukumar ta kuma cafke wata mace mai shekara 40 ɗauke da sinƙi 70 na tabar wiwi a Jihar Imo, da wasu mutum biyu da aka kama da lita 39 na ƙwayar Skuchies da kuma Tramadol da Rophynol.

An kuma cafke wani babban dilan ƙwaya a yankin Okitipup na Jihar Ondo, wanda aka ƙwace hodar iblis da Heroin da Methamphetamine da Colorado da kuma Loud a hannunsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *