Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kama wani limamim coci da wasu mutane da ake zargi da bayar da bindigogi ga ‘yan fashi da makami da sauran masu aikata laifuka a jihar Filato, jihar Kaduna da wani bangare na jihar Nasarawa da sauransu.
Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a makon jiya a Abuja.
A cewarsa, waɗanda ake zargin ‘yan ƙungiyar ‘yan bindiga ne a jihar Filato, jami’an ‘yan sandan farin kaya (IRT) sun kama su a unguwanni daban-daban a garin Jos.
Ya ce a yayin farmakin an gano tarin makamai da alburusai, kuma an kuɓutar da mutane da dama da aka yi garkuwa da su.
Rundunar ta IRT, a cewar mai magana da yawun rundunar ta kai ga cafke Joseph Tata mai shekaru 33, wanda aka fi sani da Muazu daga ƙauyen Zumu da ke karamar hukumar Mikang a jihar Filato. An kama shi daga baya ya kai ga kama wasu ƙarin mutane huɗu: ɓictor Ali-Pam, 33; Abua Yusuf; Bako Isa; da Salamatu Ilya, 34, macen da ake zargi da zama a Jos.
Dangane da wannan nasarar, jami’an IRT sun kama wasu mutane biyu a ranar 28 ga watan Janairu, 2025: Musa Ari daga Tambegua, jihar Kaduna, da Britus Tom daga ɓom, jihar Filato.
Adejobi ya ce, binciken da aka yi wa motarsu, wata motar kirar ɓolkswagen mai kala ja, ta gano wasu boyayyun makaman yaki da ta hada da: bindigogi ƙirar AK-47 guda 8 da alburusan su.
Ya kuma bayyana cewa suna kan hanyar kai makaman ne ga ’yan ta’adda da ke aiki a Filato da Kaduna da kewaye a lokacin da aka kama su.
Ya ce, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya amince da karɓar bindigogin daga hannun wani fitaccen mai yin katsalandan da aka fi sani da Gyan, wanda a halin yanzu yake tsare kuma ana kyautata zaton yana garin ɓom na jihar Filato.
A wani labarin kuma, an kama Amos Sunday Gyan da laifin mallakar wata kƙaramar bindiga. Ya yi ikirarin cewa ya gano makamin ne a wani gidan haya amma ya kasa kai rahoto ga hukuma.
Har ila yau, an kama wani dattijo mai shekaru 60, Alhaji Tanko na Shrinaka, Jihar Filato da laifin mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba.
Rundunar ‘yan sandan ta bayar da rahoton kwato da ceto da aka samu a yayin samamen: bindigogi iri-iri 172; harsashi guda 3,174 na nau’i daban-daban; da kuma motocin sata 115, yayin da aka ceto mutane 387 da aka yi garkuwa da su.