An damƙe mutane tara bisa zarginsu da hannu a ruftawar gini a Changsha

Daga CMG HAUSA

Yan sanda sun kama mutane tara da ake zargi da hannu a ruftawar wani gini da wasu mutane suka gina da kansu a Changsha, babban birnin lardin Hunan, dake tsakiyar ƙasar Sin, jami’an ‘yan sandan yankin sun tabbatar a yau Lahadi.

Daga cikin mutanen da aka kama sun haɗa da mamallakin gidan, da kuma mutanen da suka jagoranci aikin ginin.

Ginin beni ne mai hawa shidda a gundumar Wangcheng, mai faɗin murabba’in mita 700, ya rikito da misalin karfe 12:24 na ranar Juma’a.

Kawo yanzu, mutane biyar sun tsira da ransu bayan da aka zaƙulo su daga cikin burabuzan ginin, kana jami’an aikin ceto suna ci gaba da aikin gano mutane da dama da suka bace.

Fassarwa: Ahmad