An damke ɗan shekara 12 da ya yi garkuwa da ‘yar shekara uku a Bauchi

Daga BASHIR ISAH

‘Yan Sanda a Jihar Bauchi sun damke wani yaro ɗan shekara 12 a yankin Magama Gumau kan zargin yin garkuwa da wata yarinya ‘yar shekara 3.

Bayanan da ‘yan sandan suka samu sun nuna, a ranar 23 ga Nuwamban 2022, wani mai shago da ke yankin, Yahaya Sale, ya samu kiran waya a kan ana bukatar kuɗi N150,000 daga hannunsa kafin a sako ‘yarsa ‘yar shekara 3 da aka yi garkuwa da ita a yankin.

Binciken ‘yan sanda ya gano yaron ya yaudari yarinyar zuwa wani kangon gini ne sannan ya kira mahaifin yarinyar a waya a kan ya kawo kuɗi.

An ce jin haka sai mahaifin yarinyar ya katse kira, daga nan bai sake daga kiran dyaron ba.

Daga bisani aka ce, sai mahaifin ya nemi wata waya daban ya kira lambar inda a nan ya gano yaron ta muryarsa har da ambaton sunansa.

Jin haka aka ce sai yaron ya sha jinin jikinsa ganin cewa mahaifin yarinyar ya gano shi.

Daga nan sai ya gaggauta ɗaukar yarinyar zuwa gidansu inda ya faɗa wa mutanenta cewa ya hange ta ne tana kuka a can kusa da filin ƙwallo. Jin haka aka ce sai ‘yan gidan suka kai rahoto wajen ‘yan sanda.

Da yake amsa tambayoyin ‘yan sanda, yaron ya ce daga Kano yake, kasuwanci ne ya kawo shi Bauchi tare da kanensa.

Ya ce da sana’ar sayar da soyayyar doya da yake yi a Magama Gumau ya tara kuɗin da sayi waya.

Binciken ‘yan sandan ya gano wanda ake zargin ya san a yi garkuwa da mutum ne tun bayan da aka yi garkuwa da wani abokinsa a Kano wanda sai da aka biya fansa kafin aka sako shi.

Haka nan, yaron ya faɗa wa ‘yan sanda cewa, da a ce ya yi nasara, ya yi niyar yin amfani da kuɗin ne wajen sayen sutura da wayoyi.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed wakil Anipr, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Tare da ba da tabbacin za su zurfa bincike sannan su sanar da jama’a halin da ake ciki, kana daga bisani a miƙa batun ga kotu.

Daga nan, jami’in ya nusar da iyaye kan su sanya ido a kan ‘ya’yansu yadda ya kamata, kana su kula da irin abokan da suke zirga-zirga da su a kowane lokaci.