Daga USMAN KAROFI
A yau, 26 ga Maris, 2025, Gwamnatin Tarayya ta fara biyan matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) sabon albashi na ₦77,000 a kowane wata. Wannan na zuwa bayan amincewar gwamnati a watan Satumba na shekarar da ta gabata don ƙara kuɗin alawus daga ₦33,000 zuwa ₦77,000, bisa ga dokar sabon mafi ƙarancin albashi da aka sabunta a 2024.
Wasu matasa masu yi wa ƙasa hidima sun tabbatar da samun kuɗin a shafukan sada zumunta, inda wasu suka wallafa hotunan shaidar shigar kuɗin a asusun ajiyarsu. Wani mai amfani da Twitter (@ToluDaniel10) ya ce:
NYSC na biyan ₦77,000 ga matasa masu bautar ƙasa. Idan kuna da damar tuntuɓar wata yarinya, ku gode mata, da alama gwamnati ba za ta saurare ku ba dan ita ba.”
Wani mai amfani da Twitter (@fimlex2) ya yi mamakin shiru da ake yi bayan an fara biyan sabon albashin, yana mai cewa:
NYSC ta biya ₦77,000 ga kowane matashi, amma sai ga shi babu hayaniya kamar yadda ake yi idan sun gaza biyan.”
Kazalika, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa za a biya duk wani bashin da ake bin masu yi wa ƙasa hidima. Ministan ci gaban matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana cewa ana aiki don ganin duk wanda bai samu ba an biya shi.
Wannan ƙarin alawus na da nufin rage wa matasa wahala da kuma tallafa musu a rayuwar su ta yau da kullum.