An fara haska fim ɗin ‘Hikima’ a sinima

Masu kallo sun fara tantance finafinan da za su kalla – Alhaji Sheshe

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Fitaccen furodusa a masana’antar finafinai ta Kannywwod Mustapha Ahmad, wanda aka fi sani da Alhaji Sheshe, ya bayyana sauyin zamani da aka samu a duniyar fim shine ya kai su ga sauya akalar aikin su zuwa aiki mai nagarta, domin a yi tafiya irin yadda ake gudanar da harkar kasuwancin fim a duniya. Don haka ne ma su ka shirya fim ɗin ‘Hikima’ wanda yake ɗauke da labari mai ban al’ajabi.

Mustapha Ahmad ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Manhaja a lokacin da ake haska fim ɗin a sinima, wanda mu ka fara tambayar sa dalilin tsawon lokacin da fim ɗin ya ɗauka ba tare da an sake shi ba, in da ya bayyana cewar, “To shi daman wannan fim ɗin mun yi shi da wata manufa, don haka ne ma aka ga ba mu sake shi da wuri ba. Manufar kuwa ita ce, mu na son finafinan Kannywwod su rinƙa shiga wasu manhajoji da suke ‘International’, irin su Amazoon da sauran su, don haka duk fim ɗin da aka yi shi da irin wannan manufa, to za ka bi wasu hanyoyi domin ka ga ka cimma nasara.

“To ƙoƙarin bin waɗannan hanyoyin ne ya sa har mutane suke ganin mun ɗauki dogon lokaci ba mu sake shi ba, kuma ga shi Allah ya kawo mu lokacin da a yanzu aka fara kallon sa a sinima, kuma da yardar Allah a yanzu muna nan daf da kaiwa ga matakin da mu ke nufi, amma dai a yanzu muna gaɓar farko ta nuna shi a sinima a kalle shi don a ga irin aikin da mu ka yi. “

Ya ƙara da cewa, “Duba da yadda aikin fim ya koma a duniya, shi ya sa mu ka tsaya mu ka tsara fim wanda zai iya zuwa ko’ina a duniya, don haka duk da cewar fim ɗin Bahaushen fim ne, amma ba fim wanda shi Bahaushe ya saba kallo ba, don haka mun zo da wasu abubuwan da ba su saba ganin su ba, wanda duk wanda ya kalla zai san cewar lallai an fara samun sauyi a cikin harkar finafinan kannywwod.”

Dangane da irin kuɗin da aka kashe wajen aikin fim ɗin kuwa, mun tambaye shi ko yana ganin kwalliya za ta biya kuɗin sabulu wajen dawowar sa?

Sai ya ce, ” Gaskiya tun yanzu ma ta biya, domin mu na son mu kai masarautar wani mataki ne, to ko a yanzu za mu iya cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu, don haka sai dai burin mu na gaba, wanda kuma babban burin mu shine, mu ɗora ita masarautar a harkar kasuwancin da ta fi ta yanzu, kuma muna fatan haƙar mu za ta cimma ruwa, don haka mu ke fatan abokan sana’ar mu masu shirya finafinan Hausa su yi koyi da abin da mu ka yi, kuma za mu so su yi wanda ya fi namu ma, saboda muna son dukka a gudu tare a tsira tare. “

Daga ƙarshe ya yi kira ga masu gudanar da harkokin sana’ar su a cikin masarautar Kannywwod da su daure su yi abin da ya kamata domin a samu a kai inda a ke son a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *