An fara kaɗa kuri’a a Amurka don zaɓen sabon shugaban ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI

A yau Talata ne ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Amurka inda al’umma ke fatan samu sabon Shugaba tsakanin Donald Trump da Kamala Harris.

Harris ita ce ƴar takarar jam’iyyar Democrats bayan da shugaban ƙasar, Joe Biden ya janye daga tsayawa takarar, wadda ta kasance mai neman a bada ƴancin zubar da ciki da neman a sauƙaƙe farashin kayan abincin da na gidaje ga ma’aikata.

Trump kuma a nasa ɓangaren ya yi alƙawarin rufe kan iyaka da kuma rage kuɗin haraji da kaso mai tsoka.

Tsohon shugaban ƙasar ya kuma tsallake harin mutuwa har sau biyu a baya a lokacin da ya ke yaƙin neman zaɓe.

A halin yanzu dai kowane ɗan takara daga cikin su ya kamala yaƙin neman zaɓensa da shirin kafa sabuwar gwamnati bayan alƙawuran da suka ɗauka wa al’umma.