An fara tattara sakamakon zaɓen gwamna na Jihar Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar INEC ta fara bayyana sakamakon zaɓen gwamna na Jihar Kaduna, da aka gudanar ranar Asabar.

A ranar 18 ga watan Janairu ne al’ummar Nijeriya ke gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohi 28, da kuma na majalisar dokokin jiha a faɗin ƙasar.

Kaduna ce jiha ta uku mafi yawan al’umma a Nijeriya. Alƙaluman hukumar zaɓen ƙasar sun nuna jihar cewa na da masu rijistar zaɓe 4,335,208.

Jihar na da yawan ƙananan hukumomi 23.

Ƴan takara 14 ne ke neman maye gurbin gwamna El-Rufai a zaɓen da ke tafe.

ƘARAMAR HUKUMAR MAKARFI

APC = 25,673
PDP = 26,128
NNPP= 532
LP= 278

ƘARAMAR HUKUMAR SANGA

APC = 12,338
PDP = 13,119
NNPP= 568
LP= 2,871

ƘARAMAR HUKUMAR JABA

APC = 7,564
PDP = 14,616
LP= 2,871

ƘARAMAR HUKUMAR KAJURU

APC = 8,271
PDP = 23,115
LP= 1,773

ƘARAMAR HUKUMAR GIWA

APC = 30,773
PDP = 28,869

ƘARAMAR HUKUMAR IKARA

APC = 29,066
PDP = 28, 612

ƘARAMAR HUKUMAR KAURA

APC = 7,748
PDP = 15,108
NNPP = 818
LP = 12,950

ƘARAMAR HUKUMAR JEMA’A

APC = 19,920
PDP = 28,963
NNPP = 543
LP = 6,017