An gano akwatin tattara bayanai na biyu na jirgin saman MU5735 na ƙasar Sin da ya yi haɗari

Daga CMG HAUSA

A yau Lahadi, an gano akwatin tattara bayanai na biyu na jirgin saman fasinja na MU5735 na kamfanin jirgin saman ƙasar Sin wato China Eastern Airlines.

Jirgin saman na MU5735, wanda ya taso daga birnin Kunming zuwa Guangzhou, duk birane ne na kasar Sin, yayi hadari da yammacin ranar Litinin a yakin Guangxi Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin ƙasar Sin. Dukkan mutanen dake cikin jirgin su 132 sun mutu, kamar yadda jami’an aikin ceto suka tabbatar da hakan a ranar Asabar.

An bada sanarwar ne kwanaki shida bayan gudanar da cikakken bincike a wajen da haɗarin ya faru, da kuma duba kyamarorin bincike, da sauran na’urorin dake lura da taswirar yankuna. Kawo yanzu, an gano kwayoyin halittun mutane 120 da haɗarin ya rutsa dasu ta hanyar gwaje-gwajen.

An gano akwatin tattara bayanai na farko ne a ranar Laraba, kuma ana ci gaba da gudanar d ayyukan kwashe bayanan daga cikin akwatin farkon.

Za a gabatar da rahoton binciken farko ga hukumar kula da sifurin jiragen sama ta ƙasa da ƙasa cikin kwanaki 30, kamar yadda shugaban cibiyar binciken haɗurran jiragen sama na ƙasar Sin CAAC, Mao Yanfeng ya bayyana a ranar Juma’a.

Fassarawa: Ahmad