An gano gawar ɗan shekara uku a cikin rijiya a Kano

Daga AISHA ASAS

Jami’an kwana-kwana a jihar Kano sun gano gawar wani yaro ɗan shekara uku wanda ya faɗa a rijiya a garin Gaida da ke yankin Ƙaramar Hukumar Kumbotso a jihar.

Kamfani Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kwana-kwana na Jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan a Kano.

Abdullahi ya ce wannan al’amari ya auku ne da yammacin Larabar da ta gabata.

A cewarsa, da misalin ƙarfe 4 na yamma suka samu labari kan faɗawa rijiya da yaron ya yi, inda cikin gaggawa suka tura jami’ansu wanda a ƙarshe suka samu nasarar ciro gawar yaron.

Ya ci gaba da cewa, bayan da aka fito da gawar an miƙa ta ga mahaifin yaron, Musa Isa, don yi mata jana’iza.

Abdullahi ya ce ana kan bincike domin gano dalilin faɗawar marigayin cikin rijiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *