An gano kadarorin naira tiriliyan 1.49 a Dubai, mallakar ƴan Najeriya ciki har da El-Rufa’i da ƴar Atiku da Baba Ahmad da sauransu

Daga Edita

Cikin shekaru huɗu, adadin ƴan siyasar da asirin su ya tuno a Najeriya (PEPs), ya ninka inda a shekarar 2020, bincike ya nuna cewa gidaje 800 da ƙudinsu ya kai dala miliyan 400 a Dubai da ke ƙasar Haɗaɗdiyar Daular Larabawa mallakan ƴan Najeriya ne wanda kuma a shekarar 2024 sun kai kimanin mutum 1,600 wanda kuɗin su ya kai kusan dala biliyan 1.

Tawagar aikin bincike kan rahoton laifukan sata da almundahana da dukiyar al’umma (OCCRP), ita ce ta gudanar da binciken tare da gidajen jaridu guda 70 yayin da Jaridar ‘Economy Post’ ta wakilci Najeriya.

Rahoton ya ce, bayan ƴan ƙasar Indiya, ƴan Najeriya ne ke kan gaba wajen sayan kadarori musamman gidaje a birnin Dubai.

Jaridar ‘Daily Post’ ta ce, wani bincike da ‘BusinessDay’ ya yi kan batun ya ce, banda PEPs, akwai manyan ma’aikatan tsaro, da ma’aikatun gwamnati, da waɗanda ke da alaƙa da gwamnati tare da iyalansu da ke da gidaje a ƙasar inda ta ce kaso 88 na kadarori a Dubai, mallakar ƴan Najeriya ne.

Rahoton ya ƙara da cewa inda waɗannan kadarori su ke sun haɗa da Burj Khalifa, ginin da ya fi kowane tsawo a duniya da Marsa Dubai da Al-Merkadh da Palm Jumeirah da Wadi Al Safa da Madinat Al Mataar da Nada Al shiba.. da sauransu.

Sannan, binciken ya gano cewa, kadarorin da aka yi ma rijista da sunan mace, to na namiji ne, haka idan an yi da na namiji, to na mace ce.

Jaridar ta kuma ce, binciken bai samo hujjar cewa mamallakan sun mallaki kadarorin da kuɗi na sata ko kuɗin ƙasa ba a yanzu.

Sunayen waɗanda rahoton ya zayano sun haɗa da; Atiku Abubakar, da gida mai kuɗin dala miliyan 1.23 da ƴarsa mai gidaje biyu da kuɗinsu ya kai sama da dala dubu 393; sai Lateef Fagbemi, Antoni Janar na ƙasa kuma ministan shari’a da kadarar sama da dala dubu 85; sai El-Rufa’i, tsohon gwamnan Kaduna da ke da gidan da kuɗinsa ya kai sama dala dubu 193.

Sauran sun haɗa da; Yusuf Datti Baba Ahmad mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP a zaɓe 2023 da kadarorin dala miliyan 2.28, sai Attahiru Bafarawa da kadarori guda 7 da suka kai kimanin dala miliyan 1.48, sai Ifanyi Uba da na dala miliyan 1.13 da aka samu ke ɗauke da sunan matarsa Uchenna Uba.

Rahoton ya cigaba da zayyano sunayen mutane kamar haka; Ahmed Maƙarfi, tsohon gwamnan Jihar Kaduna da kadarar sama da dala dubu dari 822; Marigayi Tafa Balogun, tsohon Sufeta Janar na Ƴan sandan Najeriya da kadarar sama da dala miliyan 1.

Sauran mutane a jadawalin sun haɗa da; Mbu Joseph da Ahmadu Ali, tsohon shugaban PDP da aka danganta dukiyar da ƴarsa Nneamaka Ali da Maina Aji Lawan tsohon gwamnan Jihar Barno da Ashe Ahmadu Muazu da Christabel Bentu da Isa Mahmoud Nuhu da Salisu Abdullahi Yushau da Mohammed Sidi Sani da Hadiza Ali Sheriff da Nenadi Usman da Bobboi Kaigama da Jimoh Ibrahim da Ike Ekweremadu da Orji Uzo Kalu da Jeremiah Usaini da Osita Chidoka da Olisa Metuh da Abdussalami Abubakar da Hassan Ardo Tukur da Adeyemi Ikuforiji da kuma Dan Etete.