An gano mutum 51ɗauke da cutar tarin fuka a Binuwai

Daga UMAR M. GOMBE

Dr Chubby Eze daga gidauniyar KNCV Foundation mai zaman kanta, ya ce mutum 51 ne aka tabbatar sun kamu da cutar tarin fuka (TB) daga cikin mutum 609 da aka yi musu gwaji a Makurdi babban birnin jihar Binuwai.

Eze ya bayyana haka ne sa’ilin da yake amsa tambayoyin manema a Makurɗi a Juma’ar da ta gabata, tare da cewa an ɗauki samfurin mutane daga sassan ƙananan hukumomin jihar aka tafi da su cibiyoyin gwaji.

Mr Dominic Alamkah wanda ke da hannu a shirin gwajin, ya shawarci waɗanda aka gano ɗauke da cutar da su tabbatar sun sha magungunan da aka ba su yadda ya kamata.

Ya ce duk wanda ya kiyaye dokoki ya yi amfani da magungunansa bisa ƙa’ida zai samu sassaucin cutar. Kazalika, ya shawarce su da su yi ƙoƙarin bin matakan kariya daga barin cutar don amfanin kansu.

Jami’an sun ce suna aiki tukuru wajen ganin sun raba jihar Binuwai da cutar TB baki ɗaya wanda hakan ne ma ya sa suka shirya wannan shiri na bada maganin ga waɗanda aka gano suna ɗauke da cutar a jihar.

Sun ce shirin nasu mai manufofi biyu ne, wato gwada mutane don gano masu ɗauke da cutar da kuma wayar da kan jama’a game da ita. Don haka suka yi kira ga al’umma baki ɗaya kan buƙatar da ke akwai a haɗa hannu wajen yaƙi da cutar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Breakthrough Action-Nigeria, KNCV Foundation da kuma Apin Public Health Initiative sun haɗa kai wajen gudanar da shirin ne domin aiwatar da gwaje-gwajen cutar TB ga mutane.