Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) Gianni Infantino, ya ce babu tabbacin hukumomin ƙwallon ƙafar ƙasashe da suka sami gurbi a gasar lashe kofin duniya ta mata da aka fara a ranar Alhamis, da ƙasashen Australia da New Zealand za su ɗauki nauyi, za su iya kammala rabawa ’yan wasansu kuɗaɗen da ya kamata a ba su.
Kowace ‘yar wasa da za ta fafata a gasar za ta samu dala dubu 30, wanda a baya hukumar ta ce za ta tura musu kuɗinsu kai tsaye, ba sai ya bi ta hannun hukumomin ƙasashensu ba, sai dai hakan ba ta samu ba.
Hukumar FIFA ta ware dala miliyan ɗari da 10 don rabawa ’yan wasan ƙasashen 32 da suka samu gurbi a gasar ta bana, ƙari akan dala miliyan 30 da ta ware wa gasar ta shekarar 2019 da kuma dala miliyan 15 a gasar ta shekarar 2015.
A gasar lashe kofin duniya ta maza da aka yi a shekarar da ta gabata a Ƙatar, hukumar FIFA ta rabawa ’yan wasan ƙasashe 32 kyautar dala miliyan 440.
Infantino ya sha alwashin ganin hukumar ta dai-daita yawan kuɗaɗen da ’yan wasa maza da mata ke samu a gasar lashe kofin duniya na ɓangarorin da ke tafe a shekarun 2026 da kuma 2027.
A jiya ne dai ƙasashen Australia da New Zealand su ka buɗe gasar, inda Australia ta kara da Norway ita kuma New Zealand ta kara da Ireland.